Osinbajo ya yabawa Saraki a kan wani abu daya da yayi a kan mulki

Osinbajo ya yabawa Saraki a kan wani abu daya da yayi a kan mulki

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu ya yi godiya ga Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki akan rashin darewa kujerar shugaban kasa kafin bikin rantsar da su.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a wani liyafar cin abincin dare da aka shirya domin karrama Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi kansa a fadar Shugaban kasa..

A ranar Laraba ne dai aka rantsar da Buhari da Osinbajo karo na biyu .

Shugaban kasar wanda zai bar kasar zuwa Makkah, kasar Saudiyya a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu domin halartan taron OIC, ya samu wakilcin mataimakin Shugaban kasa a wajen liyafar.

Osinbajo ya yabawa Saraki a kan wani abu daya da yayi a kan mulki

Osinbajo ya yabawa Saraki a kan wani abu daya da yayi a kan mulki
Source: UGC

“Wani abun al’ajabi ya faru a safiyar yau, ni lauya ne kuma malamin shari’a kuma na kan gwaji da tambaya ta sigar doka.

“Da misalin karfe 12 da minti daya na daren jiya, zuwa 10:30 na safiyar yau 29 ga watan Mayu lokacin da aka rantsar damu a karo na biyu babu Shugaban kasa ko mataimakin Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta fara farautar tsoffin gwamnoni masu barin gado

“Abun mamaki babu wani akasi da aka samu, komai na nan yadda yake, idan ace wani lamari zai taso, Shugaban majalisar dattawa ne zai yi aiki a matsayin Shugaban kasa.

“Don haka, lokacin da na iso Eagle Square da safen nan, wasu za su lura cewa Shugaban majalisar dattawa dani muna ta barkwanci.

“Yace dani cikin barkwanci, gwara fa kayi a hankali kaa san nine mukaddashin Shugaban kasa yanzu, don haka, muna godiya ga Shugaban majalisar dattawa da bai yi wani abun ashha ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel