EFCC ta fara farautar tsoffin gwamnoni masu barin gado

EFCC ta fara farautar tsoffin gwamnoni masu barin gado

Bayan cikar wa’adin mulkin wasu daga cikin gwamnonin kasar, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta fara bibiyar wadanda ke makale da guntun kashi a tsuliyarsu.

Ana dai zargin wasu daga cikin gwamnoni masu barin gado da laifin cin hanci da rashawa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wani jami’in EFCC ya sanar da cewa, gwamnonin da ke da zargin rashawa sun san kansu don haka shawartarsu da su gabatar da kansu ga hukumar domin bincike a yanzu da suka sauka daga mulki.

EFCC ta fara farautar tsoffin gwamnoni masu barin gado

EFCC ta fara farautar tsoffin gwamnoni masu barin gado
Source: Depositphotos

An tattaro cewa a yanzu haka hukumar ta dauki dukkan matakan da ya dace don ganin cewa gwamna ne, mataimaki ko ma wane ne bai gudu ya bar kasar ba bayan bayar da ragamar mulki.

KU KARANTA KUMA: Ndume ya sake ragargazar shugabannin APC kan shugabancin majalisa

A wani labarin kuma, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa dayi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa duk duniya babu kasar dake yaki da rashawa kamar Najeriya, kamar yadda ya shaida ma jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu yayin da yake tattaunawa a bayan fagge a bikin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu daya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel