Ndume ya sake ragargazar shugabannin APC kan shugabancin majalisa

Ndume ya sake ragargazar shugabannin APC kan shugabancin majalisa

Tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa kuma dan takarar kujerar Shugaban majalisa na tara, Sanata Ali Ndume, ya sake caccakar shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan shugabancin majalisa.

Ndume ya bayyana cewa yadda shugabannin jam’iyyar APC suka nuna goyon baya ga dan takara daya, karya doka ne, da kuma tsantsar rashin adalci karara ga sauran masu sha’awar tsayawa takara.

Yayin da Ndume ya ce shugabannin APC sun karya tsarin dimokradiyya, sai dai kuma ya kara jaddada karfin guiwar da ya ce ya ke da ita na yin nasara a zaben, duk kuwa da cewa shugabannin APC Ahmed Lawan suke goyon baya.

Ndume ya sake ragargazar shugabannin APC kan shugabancin majalisa

Ndume ya sake ragargazar shugabannin APC kan shugabancin majalisa
Source: UGC

Sanatan ya ce APC ta karya dokar kasa, kuma ta yi rashin adalci, hakan ne yasa ya fito domin ya karya wannan rashin adalci da karfa-karfar da APC ke neman yi wa Majalisar Dattawa, inda aka maida dattawan wasu kananan yara.

Ndume wanda wannan ne zangon sa na uku da zai shiga a Majalisar Dattawa, tun can baya ya ce ba za su yarda a yi wa Majalisa dauki-dora ba, kuma ko an dora, za su kalubalanta, domin an kauce wa dimokradiyya kuma an karya abin da dokar kasa ta gindaya, cewa ta hanyar zabe ne kadai shugabannin majalisa za su iya hawa kan kujerar su.

KU KARANTA KUMA: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sakataren tsare-tsare na matasan APC a yankin arewa maso gabas, Aminu Makko ya bayyana cewa Sanata Danjuma Goje ne dan takarar da yafi cancanta da shugabancin majalisar dattawa na tara.

Makko wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, 29 ga watan Mayu a Abuja, ya bayyana cewa dukkanin mutanen da ke takarar kujerar, Sanata Goje ya fi su cancanta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel