Goje ne yafi dacewa da shugabancin majalisar dattawa – Jigon APC

Goje ne yafi dacewa da shugabancin majalisar dattawa – Jigon APC

- Wani jigo a kungiyar masu ruwa da tsaki na matasan APC a yankin arewa maso gabas, Aminu Makko ya bayyana cewa Sanata Danjuma Goje ne dan takarar da yafi cancanta da shugabancin majalisar dattawa

- Makko ya bayyana cewa dukkanin mutanen da ke takarar kujerar, Sanata Goje ya fi su cancanta

- Yace shugabancin majalisar dattawa karkashin Goje zai tabbatar da ci gaba mai tarin yawa a majalisar dokokin kasar

Sakataren tsare-tsare na matasan APC a yankin arewa maso gabas, Aminu Makko ya bayyana cewa Sanata Danjuma Goje ne dan takarar da yafi cancanta da shugabancin majalisar dattawa na tara.

Makko wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, 29 ga watan Mayu a Abuja, ya bayyana cewa dukkanin mutanen da ke takarar kujerar, Sanata Goje ya fi su cancanta.

Goje ne ya fi dacewa da shugabancin majalisar dattawa – Jigon APC

Goje ne ya fi dacewa da shugabancin majalisar dattawa – Jigon APC
Source: Depositphotos

A cewarsa baya ga tarin kwarewa da ya samu daga shekaru da dama a majalisa, tsohon gwamnan na jihar Gombe na da kwarewa a yadda ake gudanar da harkar majalisa ma.

KU KARANTA KUMA: Ba sandar girma Ganduje ya mikawa sabbabbin Sarakuna ba – Kwankwaso

Makko, wanda ya kasance ma’ajin kudin kungiyar matasan Najeriya na kasa, yace shugabancin majalisar dattawa karkashin Goje zai tabbatar da ci gaba mai tarin yawa a majalisar dokokin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel