Ban aiki kungiya nema min mukamin Minista ba - Jigo a APC

Ban aiki kungiya nema min mukamin Minista ba - Jigo a APC

Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Akwa Ibom, Umana Umana ya nesanta kan sa daga wata rubutu da aka wallafa na neman Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi minista.

Ana sa ran Shugaba Buhari zai zabi ministocinsa nan ba da dadewa ba bayan karbar rantsuwar fara aiki a matsayin shuagban kasa karo na biyu da ya yi a ranar Laraba.

'Yan siyasa da mukarrabansu za suyi ta kai wa da komowa a fadar shugaban kasar domin neman samun mukami.

Jigo a APC ya gwale wata kungiya da ke neman a nada shi minista

Jigo a APC ya gwale wata kungiya da ke neman a nada shi minista
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

Mr Umana, Shugaban Oil and Gas Free Zones Authority (OGFZA) ya yi wannan jawabin ne cikin sanarwar da hadiminsa, Iboro Otongaran ya fitar a ranar Laraba inda ya ce kungiyar da ke neman a bashi minista ba ta da hurumin yin magana a madadinsa.

"Muna son mu bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana da ikon zaben duk wanda ya ke so a matsayin minista a gwamnatinsa. Babu wanda ke da damar tilasta masa zaben 'yan fadarsa," kamar yadda Mr Umana ya ce a cikin sanarwar.

"Muna shawartar al'ummar Akwa Ibom da sauran jama'a suyi watsi da dukkan abinda ke cikin sakon."

Mr Umana, ya rike mukamin tsohon sakataren gwamnatin jihar Akwa Ibom kuma shine dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben 2015 a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel