Wurare hudu da shugaba Buhari zai bai wa muhimmanci a wannan karon - Sani Zoro

Wurare hudu da shugaba Buhari zai bai wa muhimmanci a wannan karon - Sani Zoro

Dan majalisar wakilai na tarayya, Muhammad Sani Zoro, ya bayyana wasu wurare guda hudu da ya kamata shugaba Buhari ya bai wa muhimmanci a wannan sabuwar gwamnatin ta sa da ya shiga a karo na biyu

Dan majalisar wakilai na tarayya, Muhammad Sani Zoro, ya ce akwai wurare guda hudu da ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali garesu a wannan sabuwar gwamnatin. Zoro, wanda yake shugaban kwamitin kungiyar 'yan gudun hijira na yankin arewa maso gabas, ya ce shugaban kasar dole ya mayar da hankali akan rikicin da yake faruwa a kasar nan, musamman a yankin arewa maso gabas.

Ya ce an raba miliyoyin mutane da gidajen su saboda matsalar tsaro da ake fama da ita kala-kala a fadin kasar nan, saboda haka dole gwamnati ta zage dantse wurin kawo karshen matsalar a wannan karon.

Wurare hudu da shugaba Buhari zai bai wa muhimmanci a wannan karon - Sani Zoro

Wurare hudu da shugaba Buhari zai bai wa muhimmanci a wannan karon - Sani Zoro
Source: Twitter

Ya ce abu na biyu, shine gwamnati ta maida hankali wurin rikice rikicen cikin gida da ake fama dasu.

"A Najeriya ne kawai hukumar 'yan sanda bata karkashin ma'aikatar cikin gida, idan har muka yi gaggawar mayar da hukumar 'yan sanda karkashin ma'aikatar cikin gida za a samu canji ba karami ba a kasar nan."

KU KARANTA: Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Zamfara zai mayar da ma'aikata 1,400 da aka kora bakin aikinsu

Zoro ya kara da cewa dole gwamnati ta tsunduma cikin harkar sadarwa a shekaru hudun da za tayi nan gaba. Sannan ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta canja salon mulkinta wurin bayar da mukamai.

Yayin da yake bayani akan Sakataren gwamnatin tarayya na kasa, Boss Mustapha, ya ce akwai wurare da yawa da gwamnati ta mayar da kai a kansu, Zoro ya ce ya kamata gwamnati ta bayar da himma akan sababbin manufofinta a wannan karon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel