Babu abinda Buhari zai tabuka a zangon mulkisa na 2 – Buba Galadima

Babu abinda Buhari zai tabuka a zangon mulkisa na 2 – Buba Galadima

Tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa shi da kansa yafi amfani ga talakan Najeriya fiye da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buba ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu a wata hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa a ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja, inda yace babu abinda Buhari zai tabuka ma yan Najeriya a zangon mulkinsa na biyu.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ‘Sarkin garin Kano’ bai halarci taron rantsar da Ganduje karo na 2 ba

Dalilinsa na wannan batu kuwa shine, Buba yace duk mutumin da bai iya canza ministansa ko ya sallameshi ba, koda kuwa wani irin laifin aikata, koda kuwa Najeriyar gaba daya ya sata, ko kuma Buharin ma sukutum ya sata, ba zai iya aikata wani kirki ba.

Tsohon sakataren jam’iyyar CPC, Alhaji Buba Galadima ya zargi na kusa da shugaban kasa Buhari da kangeshi daga jin zahirin gaskiyar da jama’a suke fada game da gwamnatinsa, inda yace kallon makiyi suke yi masa a duk lokacin daya fada ma gwamnatin gaskiya.

Buba ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa shifa ba don mukami yake sukar gwamnatin Buhari ba, inda yace asali ma taimakon jama’an Najeriya ta hanyar tsangwamar gwamnati tare da tursasata yin abinda bata shirya yi ba don amfanin yan kasa.

A ranar Laraba, 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya karo na biyu a dandalin Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja, sai dai Janar Yakubu Gowon ne kadai ya halarci taron daga cikin tsofaffin shuwagabannin kasar Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel