Tsaro: Ganduje zai kashe N2.4bn don gina katafaren cibiyar samar da tsaro

Tsaro: Ganduje zai kashe N2.4bn don gina katafaren cibiyar samar da tsaro

Gwamnatin Jihar Kano za ta kafa cibiyar tattara bayanai na tsaro kan zunzurutun kudi Naira Biliyan 2.4 domin inganta samar da tsaro a jihar.

Gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Laraba cikin jawabin da ya yi wurin taron rantsar da shi da akayi a filin motsa jiki na Sani Abacha da ke Kano.

Ganduje ya ce za a samar da kayayakin aikin leken asiri na zamani da za su saukaka wurin samar da ingantaccen tsaro a jihar.

Ganduje zai kafa katafaren cibiyar tsaro kan kudi N2.4bn

Ganduje zai kafa katafaren cibiyar tsaro kan kudi N2.4bn
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

"Manufar mu ita ce saukaka wa 'Yan sanda da Sojoji da sauran jami'an tsaro ayyukansu a jihar. Cibiyar za ta saukaka aikin samar da tsaro. Za mu gina cibiyar ta yadda hukumomin tsaro za su iya sanya ido kan abinda bata gari ke aikatawa ta hanyar ganinsu a na'urar daukan hotuna da bidiyo na CCTV.

"Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da hankali wurin samar da tsaro kuma a shirye ta ke ta yi duk mai yiwuwa domin kare lafiya da dukiyoyin Kanawa daga bata gari," inji gwamnan.

Ya bukaci hukumomin tsaro suyi aiki tare da masu rike da sarautun gargajiya inda ya ce kirkiran sabbin masarautu hudu a gwamnatin jihar tayi sai saukaka samar da bayyanan sirri da taimakon sarakunan gargajiyan.

Gwamnan kuma ya yi kira ga sarakuna biyar na jihar su taimakawa hukumomin tsaro wurin tabbtar da tsaro a jihar a kowanne lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel