Jirgin mu yana layi zai fadi amma ko kadan ban tsorata ba - Obasanjo

Jirgin mu yana layi zai fadi amma ko kadan ban tsorata ba - Obasanjo

A ranar Laraba ne wani jirgin saman kasar Ethiopia ya kusa fadu wa yayin da yake kokarin a filin tashi da saukar jirage na Murtala Mohammed dake jihar Legas.

A cikin jirgin akwai tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, wanda ke dawowa gida Najeriya bayan ya halarci wani taro a kasar Ethiopia.

Da yake magana da manema labarai a kan hatsarin da jirgin ya kusa, Obasanjo ya ce; "ina zaune ina karatun jarida naji jirgin ya fara hajijiya yana tangal-tangal amma ni ban tashi hankali na ba, kawai sai na cigaba da karatu na."

Tsohon shugaban kasar ya ce ganin yadda bai nuna damuwarsa ba, sai nakusa da shi yake tambayar sa bai san abinda yake faruwa bane, shi kuma ya bashi amsa da cewar; "me zan iya yi a kai to?"

Jirgin mu yana layi zai fadi amma ko kadan ban tsorata ba - Obasanjo

Obasanjo
Source: UGC

Direban jirgin ya bayyana fasinjojinsa cewar ya samu rikicewa ne a lokaci na farko da ya yi kokarin sauka a filin jirgin sakamakon ruwan saman da ake yi a lokacin. Ya bayyana cewar ya fasa saukar ne bisa tsoron cewar zai iya kure titin da jirgin ke sauka ba tare da ya sani ba saboda ruwa da ya kwanta a kan kwaltar.

DUBA WANNAN: Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Ya kara da cewa hakan ne ya sa shi canja shawara tare da saka giyar tashi sama a lokacin da tayar jirgin ta kusa dira a kan kwaltar jirgin, lamarin da ya haddasa jirgin yin jijjiga da tangal-tangal da suka razana dukkan fasinjoji 390 dake cikin jirgin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel