Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles), Ahmed Musa, ya kai wa gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ziyara domin taya shi murnar sake rantsar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi a karo na biyu.

A yayin ziyarar da ya kai wa gwamnan da yammacin ranar Laraba, Ahmed Musa ya sha ruwa tare da gwamna Bagudu a gidan gwamnatin jihar Kebbi dake Birnin Kebbi.

A yau ne aka gudanar da bukukuwan rantsar da sabbin gwamnoni da aka zaba a karo na farko da na biyu da kuma shugaban kasa da mataimakinsa.

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Ahmed Musa da Bagudu

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna (Hotuna)

Ahmed Musa ya ziyarci Bagudu domin taya shi murna sake lashe zabe
Source: Twitter

Daga jihar Kebbi mai makwabtaka da Sokoto, kun ji cewar a yayin da aka gudanar da bukukuwan rantsar da sabbin gwamnoni da aka zaba a karo na farko da na biyu da kuma shugaban kasa da mataimakinsa, bikin rantsar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwa, bai samu halartar jama'ar Sokoto ba kamar yadda aka gani a wasu jihohi.

DUBA WANNAN: An kunyata Oshimhole a wurin taron rantsar da Buhari

Rahotanni sun bayyana cewar duk wanda ya shiga cikin babban birnin Sakkwato zai ga jama'a na gudanar da al'amuransu kamar yadda suka saba, wasu ma tamkar basu san cewa yaune ake bikin rantsar da zababbun shugabanni ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel