Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29

Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29

-PDP ta lashe jihohi 15 ta bar APC da 14 daga cikin jihohi 29 da aka rantsar da gwamnoni a ranar Laraba.

-A shekaru hudu da suka wuce labarin ya bambamta da yadda yake a yanzu inda a wancan lokaci APC ke kan gaba da jihohi 20 ita ko PDP na da 9 kacal.

Daga cikin gwamnoni 29 da aka rantsar a ranar Laraba, jam’iyar adawa ta PDP ta taka rawar gani inda ta doke jam’iyar APC mai mulki ta lashe kujerun jihohi 15 yayin da APC keda 14.

Shekaru hudu da suka wuce labarin ya sha bambam da yadda yake a yau, inda a wancan lokacin jam’iyar APC tayi nasarar lashe jihohi 20 inda jam’iya mai alamar lema ta samu jihohi 9 da kyar.

Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29 na gwamnonin jihohi

Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29 na gwamnonin jihohi
Source: UGC

KU KARANTA:Za’a rantsar da Buhari tare da gwamanoni 29 a yau

A iya cewa fadan cikin gida da ya barke tsakanin yan jam’iyar ta APC shi ne ya haifar da wannan rashin nasara. A daidai lokacin da zabe ke gabatowa jam’iyar ta APC na kokarin dinke barakar dake aukuwa tsakanin ‘ya ‘yanta a jihohhin Zamfara da Imo.

Duk da cewa wasu jihohin kamar Kwara da Gombe wadanda a da suke hannun PDP yanzu APC ta karbe, amma sai dai jam’iyar adawa ta PDP tayi wa APC ba zata inda ta lashe jihohi 15 cikin 29.

Ga jerin sunayen jihohi da kuma jam’iyunsu kamar yadda aka rantsar da su:

1. Abia PDP

2. Adamawa PDP

3. Akwa Ibom PDP

4. Bauchi PDP

5. Benue PDP

6. Borno APC

7. Cross River PDP

8. Delta PDP

9. Ebonyi PDP

10. Enugu PDP

11. Gombe APC

12. Imo PDP

13. Jigawa APC

14. Kaduna APC

15. Kano APC

16. Katsina APC

17. Kebbi APC

18. Kwara APC

19. Lagos APC

20. Nasarawa APC

21. Niger APC

22. Ogun APC

23. Oyo PDP

24. Plateau APC

25. Rivers PDP

26. Sokoto PDP

27. Taraba PDP

28. Yobe APC

29. Zamfara PDP

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel