Jihar Kano: Masu nakasa za suyi karatu kyauta daga firamare har digir-gir

Jihar Kano: Masu nakasa za suyi karatu kyauta daga firamare har digir-gir

- An rantsar da gwamnan jihar Kano karo na biyu

- Ya gabatar da jawabin abubuwan da zai yi a karo na biyu

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya alanta bayar da ilimi kyauta daga firamare har Digir-gir ga nakasassu a jihar Kano.

Hakazalika ya bayyana cewa za'a rage kudin makaranta ga sauran jama'a a dukkan jami'o'in jihar.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar, bayan ratsar da shi karo na biy a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2019.

KU KARANTA: Obasanjo, fasinjoji 393 sun tsallake rijiya da baya a faruwa jirgin sama

Yace: "A yau, gwamnatinmu ta sanar da ilimin firame da sakandare kyauta. Kuma za mu bayar da tallafin rage kudin makaranta ga jami'o'in gwamnati. Ga masu nakasa kuwa, ilimi kyauta ne daga firamare zuwa jami'a"

Bugu da kari, gwamnan ya sanar da bada umurnin amfani da kudi 2.4 biliyan wajen gina asibitin cutar daji a jihar Kano. Ya ce wannan asibiti zai taimala wajen rage kalubalen da masu cutar daji ke fama da shi a arewacin Najeriya."

Ganduje ya ce gwamnatinsa ta samu tallafin kudi dala milyan 500 daga hannun bankin cigabar Musulunci domin farfado da aikin noma.

A bangare guda, mun kawo muku rahoton cewa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, bai halarci taron rantsar da gwamnan jihar ba yayinda sauran sarakunan jihar irinsu sarkin Bichi, Rano, Gaya da Karaye sun samu halarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel