Buhari zai tafi taron OIC a Saudiyya ranar Alhamis

Buhari zai tafi taron OIC a Saudiyya ranar Alhamis

Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi birnin Makkah na kasar Saudiyya a ranar Alhamis domin hallartan taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC).

Sanarwar na kunshe cikin wata jawabi da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba a shafinsa na Twitter.

Shehu ya ce za a gudanar da taron karo na 14 ne a ranar Juma'a inda sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya ne mai masaukin baki.

Buhari zai tafi taron OIC a Saudiyya ranar Alhamis

Buhari zai tafi taron OIC a Saudiyya ranar Alhamis
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

Ya ce ana sa ran shugaba Buhari zai yi jawabi a wurin taron kan bukatar hadin kai tsakanin kasashen domin fuskatantar kallubalen ta'addancin da tsatsaurar ra'ayi.

"A cewar sakataren OIC, taron da aka yiwa lakabi da 'Makkah al-Mukarramah Summit: Hand in Hand toward the Future’ zai mayar da hankali ne wurin hadin kai kasashen musulmi domin magana da murya daya," inji Shehu.

"A yayin taron, Shugaban na Najeriya zai gana da wasu shugabanin kasashen duniya domin inganta hadin kai da hadin gwiwa a kan batutuwan da suka shafi kasashen."

Gwamnoni uku da su yiwa Buhari rakiya su ne, Gwamna Mohammed Abubakar Badaru (Jigawa), Gwamna Gboyega Oyetola (Osun) da Gwamna Abubakar Sani Bello (Niger) kamar yadda sanarwar ta ce.

Buhari shine shugaban Najeriya na uku da zai hallarci taron OIC bayan marigayi Umaru Yar'Adua da Goodluck Jonathan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel