Dalilin da yasa Buhari bai gabatar da jawabi ba wurin rantsar da shi ba

Dalilin da yasa Buhari bai gabatar da jawabi ba wurin rantsar da shi ba

A yau Laraba 29 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka karbi rantsuwar fara aiki sakamakon nasarar lashe zabe da su kayi a watan Fabrairun 2019.

Amma Shugaba Buhari bai yi jawabi ba a wurin taron da akayi a dandalin Eagle Square da ke Abuja saboda ranar demokradiya mai zuwa a watan Yuni.

Mukadashin Alkalin Alkalan Najeriya Justice Ibrahim Tanko Muhammad ne ya bawa shugaban kasar da mataimakinsa rantsuwar aikin.

Dalilin da yasa Buhari bai yi jawabi a wurin rantsar da shi ba

Dalilin da yasa Buhari bai yi jawabi a wurin rantsar da shi ba
Source: UGC

DUBA WANNAN: Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa Daily Trust cewa shugaban kasar zai yi jawabin kama aiki a ranar 12 ga watan Yuni wato ranar Demokradiyya.

Idab ba manta ba gwamnatin tarayya ta mayar da shagulgulan rantsar da shugaban kasar zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Majiyar ya ce shugaban kasar ba zai yi jawabinsa ba a ranar ranstar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel