Alkawurra 8 da gwamnan Katsina ya dauka yayin rantsar da shi

Alkawurra 8 da gwamnan Katsina ya dauka yayin rantsar da shi

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya dauki alkawurra takwas na wasu ayyuka da zai yiwa jama'ar Katsina a mulkinsa karo na biyu wanda suka shafi tsaro cigaban jihar.

Masari ya yi wannan alkawarin ne yayin rantsar da shi a ranar Laraba a dandalin Peoples Square da ke Katsina.

Ya ce, ina son in yi muku alkawari a kan wasu muhimman abubuwa a wannan ranar.

Alkawurra 8 da gwamnan Katsina ya dauka yayin rantsar da shi

Alkawurra 8 da gwamnan Katsina ya dauka yayin rantsar da shi
Source: UGC

"Muhimman bangarorin da za mu mayar da hankali kai sun hada da: Saka jari a Ilimi, Kara saka jari a fanin noma, Dabbaka nasarorin da muka samu a fanin lafiya da saka jari a fannin samar da ruwa.

DUBA WANNAN: Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

"Mun kuma yi alkawarin janyo matasa cikin harkokin siyasa da kyautata aikin gwamnati, inganta alaka tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa da samar da tsaro domin cigabar jihar Katsina.

"Wannan sune alkawurran da na dauka muku kuma za muyi duk mai yiwuwa domin ganin mun cika alkawurran ta hanyar gayyatan amintattu da kwararru wadanda za su tallafa mana cika alkawurran."

Ya ce wannan ne hanyar da za a bi domin tabbatar da nasarorin da aka samu a baya tare da samun sakamako cikin gaggawa a yayin da jihar ke ciga mataki na gaba wato Next Level.

Masari ya ce, "Ina son ganin jihar da ke da cikaken tsaro tare da isashen arziki da al'umma masu rayuwa cikin farin ciki da walwala.

"Fata ne itace Katsina da zama jihar da za tayi hannun riga da talauci. Hakan abu mai yiwuwa ne amma sai mun mayar da hankali wurin aiki babu kama hannun yaro cikin shekaru hudu masu zuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel