A karo na biyu an sake rantsar da gwamna Masari a jihar Katsina

A karo na biyu an sake rantsar da gwamna Masari a jihar Katsina

Da misalin karfe 11.15 na safiyar yau ta Laraba, 29 ga watan Mayun 2019, aka sake rantsar da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari tare da mataimakin sa, Mannir Yakubu a wani sabon wa'adin gwamnati karo na biyu.

Lauyan koli na jihar Katsina, Jastis Musa Danladi, shi ne ya rantsar da gwamna Masari tare da mataimakin sa a sabuwar harabar taro ta dandalin al'umma watau Peoples Square dake gaban fadar gwamnatin jihar Katsina.

Gwamna Masari yayin da ya kai wa shugaba Buhari koken rashin tsaro a jihar Katsina

Gwamna Masari yayin da ya kai wa shugaba Buhari koken rashin tsaro a jihar Katsina
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, an takaice gudanar da wani babban shagali a taron na rantsuwa domin nuna juyayin mutuwar wadanda ta'addancin 'yan baranda ya salwantar da rayukan su musamman a karamar hukumar Batsari da kuma wasu kananan hukumomi na jihar.

Shakka babu majiyar mua ta ruwaito cewa, Sarkin Katsina, Mai Martaba Abdulmuminu Kabir Usman tare da takwaran sa na garin Daura, Alhaji Umar Farouk, sun halarci taron rantsar da gwamna Masari a wa'adin gwamnatin sa karo na biyu.

Gwamna Masari yayin bayyana damuwar sa kan annobar rashin tsaro dake neman zama ruwan dare a jihar, ya yi kira na neman hukumomin tsaro da su tashi su farga tare da kiran daukacin al'ummar akan dukufa wajen kwarara addu'o'i na yalwatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KARANTA KUMA: An rantsar da gwamnan Kebbi a karo na biyu

Cikin yakini gwamna Masari yayin misalta wa'adin gwamnatin sa na biyu da akidar sake zani na dawo da martabar jihar Katsina, ya sha alwashin cewa zai gudanar da sabon mulkin sa cikin mafi koluluwar tsoron Mahallici wajen tabbatar gaskiya da kuma adalci.

Kazalika gwamna Masari ya ce gwamnatin sa ba za ta gushe ba wajen ci gaba da bayar da gudunmuwa da tallafi na goyon bayan hukumomin tsaro a yayin da suka daura damarar inganta tsaro a fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel