Yanzu-yanzu: Obasanjo, fasinjoji 393 sun tsallake rijiya da baya a faruwa jirgin sama

Yanzu-yanzu: Obasanjo, fasinjoji 393 sun tsallake rijiya da baya a faruwa jirgin sama

Tsohon shugaban kasa, Olusegu Obasanjo, ya tsallake rijiya da baya a wani abu da ya faru da ka iya zama hatsarin jirgi a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, a filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Legas.

Game da rahoton NAN, tsohon shugaban kasa tare dwasu fasinjoji 393 da ke jirgin da ya kasa sauka a filin jirgin.

Jirgin mai lamba, ET-901, ya tashi daga filin jirgin saman Bole dake Addis Ababa, kasar Habasha misalin karfe 7 na safe.

KU KARANTA: An rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, amma an fita dashi saboda rashin lafiya

Wani mai rahoton NAN wanda ke cikin jirgin ya bayyana cewa bayan kimanin sa'o'i shida a sama daga Habasha zuwa Najeriya, jirgin ta kasa sauka a Legas saboda ruwan sama da iskan da akayi a Legas.

Domin gudun hadari, sai direban jirgin ya ki sauka kawai ya zarce wanda hakan ya tayar hankalin fasinjojin da ke cikin jirgin.

Bayan yawo a cikin birnin Legas zuwa wajajen jihar Ogun na tsawon kimanin mintuna 20, jirgin ya sauka kuma babu wanda ya samu rauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel