Babu abin da ke nuna cewa jama’a za su shana a #NextLevel - Inji Hanga

Babu abin da ke nuna cewa jama’a za su shana a #NextLevel - Inji Hanga

Mun ji cewa Rufa’i Hanga wanda yana cikin manyan kusoshin tafiyar shugaba Muhammadu Buhari a da, ya koka da mulkin APC a lokacin da yayi wata doguwar hira da jaridar The Sun.

Rufa’i Rufai wanda yana cikin manyan APC a baya, yace jama’a sun cire rai da gwamnatin shugaba Buhari. Hanga yake cewa babu alamun da ke nuna abubuwa za su yi kyau a Najeriya a wa’adin karshe na shugaba Buhari.

Hanga yake cewa a halin yanzu kusan komai ya sukurkuce a Najeriya musamman a sha’anin tsaro. Tsohon ‘dan majalisar dattawan kasar yake cewa lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya a mulkin jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta kori ‘Dan ta saboda marawa Atiku Abubakar baya

A hirar, Hanga ya bayyana cewa rashin sanin aiki ne ya sa shugaba Buhari ya ki tsige shugabannin hafsun sojin kasar duk da irin barnar da ake yi. Tsohon Sanatan na Kano yace abubuwa sun cabe yanzu a Arewacin kasar.

Haka zalika Hanga ya bayyana cewa Jama’an Arewa ba su amfana da kuri’un da su ke ba APC a lokacin zabe. Hanga ya kara da cewa wasu manyan APC su na tare da shugaba Buhari ne kurum saboda son zuciya da burin siyasa.

Sanatan yace Bola Tinubu ya taba fada masa baki-da-baki cewa yana goyon bayan shugaba Buhari ne saboda abin da zai samu a karshen siyasarsa ba don aikin da yake tabukawa ba, inda yace nan gaba zai fallasa komai na APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel