Bala Mohammed ya soke dukkan karin girma da nade-naden da gwamnatin APC tayi

Bala Mohammed ya soke dukkan karin girma da nade-naden da gwamnatin APC tayi

- Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya rushe dukkan nade-nade da karin girma da magabancinsa ya yi

- Wannan ya biyo bayan korafin da gwamnan ya yi na cewa an tsinduma jihar a cikin bashi da ya kai N136 biliyan

- Mohammed ya umurci sakataren gwamnatin jihar da manyan direktocin hukumomi da ma'aikatu su tabbatar an bi dokar

Sabon gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya rushe dukkan nade-nade da karin girma da canje-canjen wurin aiki da akayi tun daga ranar da aka sanar da Hukumar Zabe, INEC ta sanar da cewa ya lashe zabe.

Sabon gwamnan Bauchi ya soke dukkan nade-naden da magabacinsa ya yi

Sabon gwamnan Bauchi ya soke dukkan nade-naden da magabacinsa ya yi
Source: UGC

Bala ya bayar da sanarwar ne a ranar Laraba 29 ga watan Mayu a cikin jawabinsa bayan karbar rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan Jihar Bauchi.

Da farko, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta tarar da bashin Naira Biliyan 136 daga gwamnatin da ta shude.

DUBA WANNAN: Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

Ya ce: "Ina son tabbatar da cewa na rushe dukkan nade-naden da akayi da karin girma da canje-canjen wurin aiki har da wadanda akayi domin tayar da fitina tun daga ranar da INEC ta sanar na ci zabe.

"Kazalika, na kuma rushe dukkan kwangiloli da kyautan filaye da motocci da gidajen gwamnati da aka yi a karshen mulkin gwamnatin da ta gabata.

"A wuraren da akayi amfani da dokokin bogi kuma za muyi amfani da doka na ainihi wurin warwaren dokokin," inji gwamnan.

A cewar The Guardian, Mohammed ya umurci sakataren gwamnatin jihar da manyan jami'an hukumomi da ma'aikatun gwamnati su yi biyaya ga dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel