Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya sake nada Usman Alhaji a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da kuma Shehu Mu'azu a matsayin babban akawun jihar Kano.

Sanarwan nadin na dauke ne cikin wata jawabi da sakataren yada labarai na gwamna, Abba Anwar ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a Kano.

Ganduje ya yabawa ma'aikatan biyu bisa hidimar da su ka yiwa jihar tare da shi a mulkinsa zango na farko da ya kare a ranar Laraba.

Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

"Gwamnan ya bayar da sanarwar ne nan take bayan an rantsar da shi kan mulki karo na biyu," inji shi.

Gwamna Ganduje ya bukaci ma'aikatan biyu su aiki babu kama hannun yaro domin tabbatar da cewa wannan mulkin ya fi na baya saboda alkawurran da ya yiwa al'umma.

An rushe dukkan masu rike da mukamman siyasa na jihar amma banda wadanda ke da wa'addin aiki kamar yadda dokokin hukumomi da ma'aikatatunsu suka tanada kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel