Hukumomi 10 da Buhari bai nada direktocinsu har ya gama zangon farko

Hukumomi 10 da Buhari bai nada direktocinsu har ya gama zangon farko

A cikin sa'o'i kadan shugaba Muhammadu Buhari zai kammala mulkinsa zango na farko sannan ya shiga zango na biyu sakamakon lashe zaben shugaban kasa na watan Fabrairu 2019 da ya yi.

Duk da cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali a fannin tattalin arziki karkashin kwamitin tattalin arziki da ke mataimakin shugaban kasa Osinbajo ke jagoranta, akwai wasu abubuwa da su kayi saura.

Watanni biyu bayan rantsar da shi kan mulki a 2015, shugaban kasar ya rushe kwamitocin direktoci na hukumomi da ma'aikatun gwamnati kuma ba a maye gurbinsu ba har sai a watan Disambar 2017 inda aka nada ciyamomi 209 da mambobi 1258.

Sai dai daga bisani an gano akwai sunayen mutane biyar da suka rasu a cikin wadanda aka yiwa nadin.

Duk da hakan akwai wasu hukumomi 10 da ba nada shugabanin su ba.

Hukumomi 10 da Buhari bai nada direktocinsu har ya gama zangon farko

Hukumomi 10 da Buhari bai nada direktocinsu har ya gama zangon farko
Source: UGC

Hukumomin su ne:

1. Hukumar rarraba wutan lantar 'Transmission Company of Nigeria' (TCN)

2. Hukumar 'Nigerian Electricity Liability Management Company' (NELMCO)

3. Hukumar 'Nigerian Electricity Management Services Agency' (NEMSA)

4. Hukumar Kwastam 'Nigeria Customs Services' (NCS)

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun fara binciken mutuwar hadimin Gwamna Shettima a gidan gwamnati

5. Hukumar tattara haraji na kasa 'Federal Inland Revenue Service' (FIRS)

6. Hukumar 'Securities and Exchange Commission' (SEC)

7. Hukumar Fansho na kasa 'Pension Commission of Nigeria' (PenCom)

8. Hukumar masu hada magunguna na kasa 'Pharmaceuticall Council of Nigeria' (PCN)

9. Hukumar 'National Institute for Pharmaceuticall Research and Development' (NIPRD)

10. Hukumar 'National Power Training Institute of Nigeria' (NAPTIN)

Kwamitocin suna gudanar da muhimman aiki wurin tafiyar da ayyukan hukumomin da suke yiwa jagoranci misali a NCS, kwamitin ce da alhakin nadin mukami, yiwa ma'aikata karin girma, ladabtar da wadanda aka samu da laifi da kuma yin tsare-tsare a hukumar.

A bangaren SEC kuma, kwamitin ce ta ke da alhakin yin tsare-tsare da dokoki a kasuwan hannun jari. Kwamitin ne kuma ke da alhakin nada masu binciken kudi, amince da kasafin kudin hukumar, kafa ofisoshi da sauran abubuwa da za su taimakawa hukumar cimma manufofin ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel