Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Gombe ya rusa dukkan kwangiloli da nade-naden da Dakwambo ya bayar na karshe

Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Gombe ya rusa dukkan kwangiloli da nade-naden da Dakwambo ya bayar na karshe

- Farawa da iyawa, sabon gwamnan Gombe ya bi takan magabacinsa

- Ya dakatad da dukkan nade-nade da tsohon gwamnan yayi tun bayan zaben 9 ga Maris

Jim kadan bayan ranstar da shi a matsayin sabon zababben gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yayha AbdulKadir, ya sanar da cewa ya soke dukkan nade-nade, kwangiloli, filaye da gwamna mai barin gado, Ibrahim Dankwambo, yayi daga ranar 10 ga Maris, 2019 zuwa yanzu.

Kana sabon gwamnan ya bayyana cewa zai sake dubi kan sabbin makarantun gaba da sakandaren da gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo tayi bayan nazari kan yiwuwan tafiyar da su dubi ga irin basussukan da aka bari na sama da N110 biliyan.

Ya yiwa alkawarin magance matsalolin da ya dukufar da ma'aikatun gwamnatin jihar ta hanyar dubi cikin jin dadin ma'aikata, karin girma da alawus.

KU KARANTA: An rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, amma an fita dashi saboda rashin lafiya

Inuwa Yahya ya kara da cewa zai gudanar da gwamnatinsa ta hanyar bude kofa ga kowa ya kawo korafe-korafe ko shawari masu kyau.

Hakazalika ya umurci dukkan sakatarorin kanana hukumomi 11 su dau ragamar mulkin kananan hukumominsu kafin nada sabbin shugabannin rikon kwarya ko zaben shugabanninsu.

Amma, gwamna mai barin gado, Ibrahim Dankwambo, bai halarci wannan taron rantsarwa ba kuma ba'a bada wani bayani kan haka ba.

Mun kawo muku rahoton cewa An baza jami’an tsaro a ciki da wajen babban filin wasan Pantami a Gombe a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, yayin da ake gudanar da bikin rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin zababben gwamnan karo na hudu a mulkin damukardiyya a jihar Gombe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel