Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana kadarar sa

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana kadarar sa

Bisa tanadin kotun tabbatar da da'ar ma'aikata da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya mika takardun shaidar bayyana kadarar da ya mallaka a duniya.

Hakan na zuwa ne gabanin rantsar da Osinbajo a matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da aka gudanar a ranar Laraba 29 ga watan Mayun 2019 cikin harabar filin taro na kasa Eagle Square dake garin Abuja.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana kadarar sa

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana kadarar sa
Source: UGC

Babban hadimi na musamman akan hulda da al'umma da kuma kafofin sadarwa, Laolu Akande, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a daren Talatar da ta gabata.

Mika takardun shaidar bayyana kadarori da kuma dukiya da Osinbajo ya mallaka na zuwa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ta sa kadarar a bisa tanadi na hukunce-hukuncen doka.

KARANTA KUMA: Kakakin Majalisar Imo ya yi murabus

Tamkar yadda ta kasance a gare sa da kuma shugaban kasa Buhari a shekarar 2015, babu wani bambamci a yanzu kan kadarar da mataimakin shugaban kasar ya mallaka duba da yadda bai samu karuwar wata dukiya ta gida, asusun ajiya, gona ko kuma hannun jari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel