An kunyata Oshiomhole saboda saba ka'ida a wurin rantsar da Buhari

An kunyata Oshiomhole saboda saba ka'ida a wurin rantsar da Buhari

- A ranar Laraba ne ake sake rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu

- Bikin rantsuwar na gudana ne a jihohi 29 na kasar nan da ake rantsar da gwamnoni a karo na farko ko kuma na biyu

- Bisa al'ada, akwai tsari da ka'idoji da manyan jami'an gwamnati da manyan baki ke bi a wajen rantsar da shugaban kasa

An kunyata shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, bayan ya tsaya a tsakanin mukaddashin alkalin alkalai na kasa, Ibrahim Muhammad, da shugabannin rundunonin tsaro a wurin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Laraba.

Shugaban jam'iyyar ya shiga sahun mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Obasanjo, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara da shugabannin rundunar tsaro yayin jiran isowar shugaban kasa filin taro na 'Eagle Square' a Abuja.

An kunyata Oshiomhole saboda saba ka'ida a wurin rantsar da Buhari

Wurin rantsar da Buhari
Source: UGC

Ganin hakan ne sai wani jami'in soji ya tunkari Oshiomhole a inda yake tsaye, bayan wata 'yar takaitacciyar tattauna wa ne sai Oshiomhole ya canja wurin da ya tsaya farko, a yayinda babban hafsan rundunar sojoji ta kasa, Abayomi Olonisakin, ya maye gurbin da Oshiomhole ya bari.

DUBA WANNAN: Daga Obasanjo zuwa Buhari: Abu 4 da ake tuna wa a gwamnatin kowannen su

Duk da ya cigaba da tsaiwa a kan layin, Oshiomhole ya koma tsakanin shugaban rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel