Allah kadai zai iya kare iyakokin Najeriya ba Yansanda ba – Shugabannin tsaro

Allah kadai zai iya kare iyakokin Najeriya ba Yansanda ba – Shugabannin tsaro

Shuwagabannin hukumomin tsaro a jiya Talata, 28 ga watan Mayu bayan ganawarsu da shugaban kasa Muhammadu Buhari, sunce Allah kadai ne mai iya tsare iyakar kasar.

A karshen ganawarsu da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja, shuwagabannin tsaron sun daura alhakin rashin tsaro a kan iyakar kasar wanda a cewarsu shine sandiyar haddasa rashin tsaro.

Shuwagabannin tsaron sun hada da; shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin, Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, Shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas da Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Abubakar Sadique.

Allah kadai zai iya kare iyakokin Najeriya ba Yansanda ba – Shugabannin tsaro

Allah kadai zai iya kare iyakokin Najeriya ba Yansanda ba – Shugabannin tsaro
Source: Twitter

Sauran shuwagabannin tsaron sun hada da, mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Monguno; Ministan tsaro, Mansur Dan- Ali, Darakta Janar na hukumar leken asiri, Ahmed Abubakar, Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu da Darakta Janar na hukumar tsaro na sirri, Yusuf Magaji Bichi inda suka shafe fiye da sa’o’i biyu suna ganawa da shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Ku yafe ni, amma zan sake daukar tsauraran matakai – El-Rufai ga mutanen Kaduna

A halin yanzu, Legit.ng ta rahoto a baya cewa a ranar Talata ne rundunar yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar damke mutane 71 cikin makonni uku da suka gabata wadanda ake zarginsu da aikata miyagun laifuka iri daban daban.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ali Janga shi ne ya shaidawa manema labarai wannan batu a babban ofishin hukumar dake jihar Kaduna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel