Ku yafe ni, amma zan sake daukar tsauraran matakai – El-Rufai ga mutanen Kaduna

Ku yafe ni, amma zan sake daukar tsauraran matakai – El-Rufai ga mutanen Kaduna

- Gwamna El-Rufai tare da sauran takwarorinsa sun dauki rantsuwar kama mulki a yau Laraba, 29 ga watan Mayu

- El-Rufai ya bukaci mutanen jihar da su yafe masa saboda nan gaba, domin zai ci gaba da daukar tsauraran hukunci

- Yace shawarar da gwamnatinsa ta yanke na sake kai Kaduna turbar inganci na bukatar tsauraran matakai da hukunci masu radadi

Yayinda aka rantsar da shi a karo na biyu, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya bukaci mutanen jihar da su yafe masa saboda nan gaba, domin zai ci gaba da daukar tsauraran hukunci.

Gwamnan a jawabin rantsar da shi da yayi a filin Murtala Mohammed Square Kaduna, wajen da aka gudanar da taron rantsarwar yace, yanke shawarar sake kai Kaduna turbar inganci da gwamnatinsa tayi na bukatar tsauraran matakai da hukunci masu radadi.

Wasu daga cikin tsauraran matakan da gwamnatin El-Rufai ta dauka a lokacin mulkinsa na farko sun hada da rushe gine-gine da suka shiga hukumkomin gwwamnati, sallaman malaman firamare 21,000 da suka gaza da kuma sallamar wasu hakimai, da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sarkin Kano Sanusi bai halarci bikin rantsar da Ganduje ba

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa a ranar Talata ne rundunar yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar damke mutane 71 cikin makonni uku da suka gabata wadanda ake zarginsu da aikata miyagun laifuka iri daban daban.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ali Janga shi ne ya shaidawa manema labarai wannan batu a babban ofishin hukumar dake jihar Kaduna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel