Bikin rantsar da shugaban kasa: Tsohon kakakin majalisar jihar Imo ya yabi Buhari

Bikin rantsar da shugaban kasa: Tsohon kakakin majalisar jihar Imo ya yabi Buhari

-Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo yace yana da kyakkyawan zato akan cewa shugaba Buhari zai kawo sauyi a kasar nan cikin wa'adin mulkinsa na biyu.

-Amaechi Nwoha yayi wannan bayanin ne bayan ya taya shugaban kasar murnar rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

Amaechi Nwoha, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo ya taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake rantsar da shi da akayi a ranar Laraba a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

Nwoha ya bayyanawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN cewa shugaban kasan ya nuna aniyarsa ta kai kasar nan mataki na gaba a bangaren cigaban tattalin arziki da kuma wadatar rayuwa.

Bikin rantsar da shugaban kasa: Tsohon kakakin majalisar jihar Imo ya yabi Buhari

Bikin rantsar da shugaban kasa: Tsohon kakakin majalisar jihar Imo ya yabi Buhari
Source: Original

KU KARANTA:Za’a rantsar da Buhari tare da gwamanoni 29 a yau

Ya kuma sake bayyana goyon bayansa ga gwamnatin Buhari inda yake cewa, shugaban zai yi aiki tukuru domin ganin bayan cin hanci a kasar nan tare da kawo tsare-tsare da zasu zame abin dogaro ga jama’a.

Kazalika, ya kara da cewa, “ Shugaban kasa mutum ne mai amana wanda ke matukar son Najeriya da kuma yan Najeriya, a don haka zai kawo cigaba cikin shekaru hudu dake tafe.

“ Hakika na yarda bisa turbar da ya daura Najeriya a kai duk da akwai masu yiwa gwamnatinsa zagon kasa a wa’adinsa na farko.” A cewar Nwoha.

Dan majalisar yace yana da yakinin cewa shugaban zai cigaba ne da ayyukan da ya faro a zangonsa na farko. Ya kuma sake yin kira ga sabbin yan majalisa ta 9 masu shigowa da su kasance masu bada kwarin guiwa ga gwamnatin tarayya domin cigaban kasar nan.

Nwoha bai mance da gwamnoni ba, yayin da yake taya su murna ya kara da basu shawarar cewa su kasance “masu bayarwa amma ba masu karba ba”, saboda a cewarsa hakan shi ne mafi kyawon ko wace gwamnati wacce ta san ya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel