Ko sama ko kasa: Ba a ga Obasanjo da Jonathan ba a wajen rantsar da Buhari

Ko sama ko kasa: Ba a ga Obasanjo da Jonathan ba a wajen rantsar da Buhari

A yau Laraba, 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a karo na biyu.

Taron rantsarwar ya samu halartan manyan mutane kama daga tsoffin shugabannin kasa, manyan yan kasuwa, masu fada aji da manyan yan siyasar kasar.

Sai dai ko sama ko kasa ba a ga tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ba a wajen taron. Koda dai dama Obasanjo dan adawa da gwamnatin Buhari ne, domin lokuta da dama ya sha caccakar tsarin mulkin Buhari.

Ko sama ko kasa: Ba a ga Obasanjo da Jonathan ba a wajen rantsar da Buhari

Ko sama ko kasa: Ba a ga Obasanjo da Jonathan ba a wajen rantsar da Buhari
Source: Depositphotos

Hakazalika, tsohon Shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan bai halarci taron ba.

Sai dai babu wani dalili da shugabannin biyu suka bayar na rashin haallaransu a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Bikin rantsar da shugaban kasa da mataimakinsa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ai halarci bikin rantsar da gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ba yayinda yake shirin kama mulki a karo na biyu.

An tattaro cewa tuni sarakuna biyu daga cikin biyar na masarautun jihar sun hallara a wajen bikin rantsarwar da ke gudana a yanzu haka a filin wasa da Sani Abacha. Sarakunan da suka hallara sune na Bichi da Rano yayinda wajen zaman na Kano, Gaya da Karaye ke nan ba kowa.

Wata majiya da ba a tabbatar bat a bayyana cewa rashin hallaran sarkin Kano saboda dalili ne na tsaro, yayinda aka bayyana cewa Sarakunan Gaya da na Karaye na a hanyarsu ta zuwa wajen taron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel