Jonathan yayi wata magana mai ratsa zuciya, yayin da Buhari yake shirin shiga Ofis a karo na biyu

Jonathan yayi wata magana mai ratsa zuciya, yayin da Buhari yake shirin shiga Ofis a karo na biyu

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi kira ga 'yan Najeriya su cigaba da gaba da hada kansu domin ciyar da kasar nan gaba

- Tsohon shugaban kasar ya taya murna ga al'ummar kasar nan wurin cika shekaru 20 da fara mulkin dimokuradiyya

- Tsohon shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya da su cigaba da hakuri, komai zai daidaita

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yayi kiraga 'yan Najeriya da su cigaba da hakuri kamar yadda kasar take cika shekaru 20 da fara mulkin farar hula.

Jonathan yayi wata magana mai ratsa zuciya, yayin da Buhari yake shirin shiga Ofis a karo na biyu

Jonathan yayi wata magana mai ratsa zuciya, yayin da Buhari yake shirin shiga Ofis a karo na biyu
Source: Twitter

A wata sanarwa da tsohon shugaban kasar ya fitar, yau Laraba 29 ga watan Mayu, yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kokarin fara sabuwar gwamnati a karo na biyu, tsohon shugaban kasar ya taya kasar murna akan cigaban da ake samu na mulkin dimokuradiyya.

Jonathan ya roki 'yan Najeriya kada su fidda rai tunda yanzu kasar tana ta fama da matsalar tsaro da rashin aikin yi ga matasa.

KU KARANTA: Mata zasu fara limancin sallah a Ghana

A halin yanzu dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana shirin fara gabatar da mulkin shi a karo na biyu, yayin da ake bikin rantsar dashi a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

Sai dai kuma wani rahoto ya nuna cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo basu halarci wurin bikin rantsar da shugaban kasar ba shi da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel