APC ta hukunta Bimbo Daramola da laifin cin amanar Jam’iyya a Ekiti

APC ta hukunta Bimbo Daramola da laifin cin amanar Jam’iyya a Ekiti

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta dakatar da wani tsohon ‘dan majalisar kasar da ta samu da laifin marawa Atiku Abubakar na jam’iyyar hamayya baya a zaben shugaban kasa da ya gabata.

APC ta dakatar da Honarabul Bimbo Daramola ne bayan tayi bincike ta gano cewa ya goyi bayan ‘dan takarar jam’iyyar adawa, Atiku Abubakar ne a zaben 2019 a maimakon shugaban kasa Buhari.

Jam’iyyar ta aikawa ‘dan majalisar takardar da ke tabbatar da dakatarwarsa ne ta hannun shugaban APC da kuma Sakataren jam’iyyar na Mazabar Ire II da ke cikin yankin Ekiti ta Arewan jihar.

KU KARANTA: Tsohon Jigon APC ya dura kan Buhari bayan ya soki Saraki

Shugaban APC na Mazabar ‘dan siyasar, watau Dipo Bejide da kuma Adeola Sefunmi, wanda shi ne Sakataren jam’iyyar ne su ka sa hannu a wannan wasika da ta fito jiya, 28 ga Watan Mayu.

Jam’iyyar ta nemi tsohon ‘dan majalisar ya zo ya kare kan-sa daga zargin sa da aka yi na taimakawa yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben bana. Daramola ya gaza kare kan na sa a gaban jam’iyya.

Ganin cewa tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyar wanda ya wakilci Ekiti ta Arewa ya gaza bayyana a gaban uwar jam’iyyar ne aka dakatar da shi daga APC saboda goyon bayan jam'iyyar PDP a fili.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel