Magance almajiranci zai kawo karshen ta’addanci da kuma yan baranda, inji Majalisar dattawa

Magance almajiranci zai kawo karshen ta’addanci da kuma yan baranda, inji Majalisar dattawa

-Sanata Lawan Ahmad yayi magana mai tsawon da kuma tasiri akan alamajiranci a yankin arewacin Najeriya inda ya nuna cewa hakan na taimakawa wurin yawaitar ta'addanci a kasar nan.

-Idan har ya zama dole sai anyi almajirancin to akwai bukatar hukumomi su shiga ciki domin ayi masa kwaskwarima, kamar yadda Lawan Ahmad ya fadi.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa sanata Lawan Ahmad shi ne yayi korafi a ranar Talata akan rashin tsaron dake addabar arewacin Najeriya inda ya danganta shi da rashin zuwa makarantar yara a yankin.

Lawan ya sake nanatawa, matsalar ta rashin tsaro zata iya habbaka zuwa ilahirin yankin arewacin idan har ba ayi yinkurin sa yara a makaranta ba.

Magance almajiranci zai kawo karshen ta’addanci da kuma yan baranda, inji Majalisar dattawa

Magance almajiranci zai kawo karshen ta’addanci da kuma yan baranda, inji Majalisar dattawa
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Madalla: Yan sanda sun kama yan ta’adda 71 a Kaduna

Dan majalisar yace, “ Idan muna yaki da ta’addanci ya zama wajibi mu dubi kafar da wannan abin ke bullowa. Masu aikata wannan aiki zaka samu yara ne yan kasa da shekara 17 wadanda yakamata a ce suna makaranta a maimakon yawon bin tituna.

“ Duk da cewa kawar da almajirancin abu ne mai matukar wahala, amma dai lokaci yayi da yakamata a duba al’amarin domin ayi masa kwaskwarima. Idan har taimakon muke son yi me yasa ba za’a killace yaran a wani wuri na musamman domin koyar dasu ilimi ba?

“ Ni a gani na, yin hakan zai taimaka kwarai da gaske wurin magance matsalolin tsaro ta hanyar kare yaran daga shiga cikin ayyukan ta’addanci. Har su iya zama silar kawo cigaban kasarmu.” A cewar Lawan.

Lawan ya sake rokon gwamnatoci a ko wane mataki, na su kaddamar da dokar hukumar ilimi ta bai daya wato UBE ta shekarar 2014 wacce ta sanya ilimi wajibi kuma kyauta ga yara kanana a fadin Najeriya.

Ana shi jawabin kan wannan maudu’i, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki cewa yayi gwamnati nada aiki ja a gabanta na ganin cewa yara sun samu ilimi mai inganci a kasar nan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel