Yanzu Yanzu: Sarkin Kano Sanusi bai halarci bikin rantsar da Ganduje ba

Yanzu Yanzu: Sarkin Kano Sanusi bai halarci bikin rantsar da Ganduje ba

Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ai halarci bikin rantsar da gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ba yayinda yake shirin kama mulki a karo na biyu.

An tattaro cewa tuni sarakuna biyu daga cikin biyar na masarautun jihar sun hallara a wajen bikin rantsarwar da ke gudana a yanzu haka a filin wasa da Sani Abacha. Sarakunan da suka hallara sune na Bichi da Rano yayinda wajen zaman na Kano, Gaya da Karaye ke nan ba kowa.

Wata majiya da ba a tabbatar bat a bayyana cewa rashin hallaran sarkin Kano saboda dalili ne na tsaro, yayinda aka bayyana cewa Sarakunan Gaya da na Karaye na a hanyarsu ta zuwa wajen taron.

Yanzu Yanzu: Sarkin Kano Sanusi bai halarci bikin rantsar da Ganduje ba

Yanzu Yanzu: Sarkin Kano Sanusi bai halarci bikin rantsar da Ganduje ba
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Bikin rantsar da shugaban kasa da mataimakinsa

Sai dai, an tattaro cewa manyan mutane da suka halarci taron sun hada da, kungiyar sojojin diflomasiyya, manyan yan kasuwa, manyan shugabannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Filin wasa na Sani Abacha ya cika ya tumbatsa da magoya bayan APC da manyan jami’anta, yayinda aka tsaurara matakan tsaro. Tuni dai Gwamna da mataimakinsa sun hallara yayinda aka fara taro ba tare da Sarkin Kano ba.

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Lagas a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, ya bayyana cewa ba zai halarci bikin rantsar da zababben gwamna, Babajide Sanwo Olu ba.

Ambode ya bayyana cewa sabon gwamnan ya cancanci jin dadin ranarsa mai cike da tarihi ba tare da shi (Ambode) ya taya shi cin garabasar daraja na wannan rana ba,jaridar Vanguard ta ruwaito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel