Yanzu Yanzu: Ba zan halarci bikin rantsar da Sanwo-Olu ba – Ambode

Yanzu Yanzu: Ba zan halarci bikin rantsar da Sanwo-Olu ba – Ambode

Gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Lagas a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, ya bayyana cewa ba zai halarci bikin rantsar da zababben gwamna, Babajide Sanwo Olu ba.

Ambode ya bayyana cewa sabon gwamnan ya cancanci jin dadin ranarsa mai cike da tarihi ba tare da shi (Ambode) ya taya shi cin garabasar daraja na wannan rana ba,jaridar Vanguard ta ruwaito.

Da yake taya zababben gwamnan mura a wani jawabi daga sakataren labaransa, Habib Auna, Ambode ya bayyana cewa a bari Sanwo-Olu ya zama taurari a wannan rana.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel