Gidauniyar Asattahir International Foundation ta ba da Tallafi ga Almajiran da aka yiwa Fyade a jihar Sokoto

Gidauniyar Asattahir International Foundation ta ba da Tallafi ga Almajiran da aka yiwa Fyade a jihar Sokoto

A cikin kokarin ta da jajircewar ta don ganin sun tallafawa wa Marayu da Yara kanana Marasa Galihu, ASATTAHIR International Foundation ta ceto kananan yara da ake ci ma zarafi ana masu fyade a Jihar Sokoto.

Wadannan yara bakowa bane face wadansu Almajirai a wata Unguwa mai suna Arkilla a cikin garin Sokoto.

an bankado cewar wanda keyiwa yaran fyaden ba wani bane face Malamin su kuma mai kula dasu.

shi da kanshi ya tabbatar da laifin da ake zargin nayiwa kananan yaran fyade wadanda suke karkashin kulawar shi.

Kwamishinan yansandan Jihar Sakwato CP Ibrahim S kaoje ne ya Halarto da wanda ake zargi da Almajiran da akayi lalata dasu a Gaban Yan Jaridu a hedikwatar yansanda ( C I D ) dake Jihar Sakwato a ranar 27 ga Mayu, 2019.

Gidauniyar Asattahir International Foundation ta ba da Tallafi ga Almajiran da aka yiwa Fyade a jihar Sokoto

Gidauniyar Asattahir International Foundation ta ba da Tallafi ga Almajiran da aka yiwa Fyade a jihar Sokoto
Source: Facebook

Hukumar Kare Hakkin Dan-Adama ta kasa (Human rihgt commission) reshen jihar Sakwato ta fara tuntubar Gidauniyar Asattahir International Foundation din domin ta taimaka wajen ceto yaran da kuma tallafa masu da kula dasu don ganin basu sake fadawa a cikin halin da suke ciki ba a cikin al'umma.

A matsayin amsa gayyatar, Gidauniyar Asattahir International Foundation tasamu tattaunawa da kwamishinan 'yan sandan Jihar Sakwato, Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta Duniya, Ma'aikatan Harkokin Lamurran Addini da ta Shari'a da sauran Ƙungiyoyin' Kare Hakkin Bil'adama tare da Musayar ra'ayi don a gano yadda za'a magance wadan su cututtuka da Maiyiwa Almajiran zasu iya samu sanadiyar fyaden da akai musu na zahiri kona badini .

Bayan tattaunawari shawarwari da tare da masu ruwa da tsaki, Kungiyar Asattahir International Foundation ta ba da kayan agaji ga wadanda aka ci zarafi su kuma ta dauki nauyin kuɗin motar da zai mayar dasu gaban Iyayen su. Kungiyar ta bayar da shawaraa ga hukumar Yan Sanda da Ma'aikatar Shari'a da su kulle Makarantar har sai an kammala bincike.

A yayin ganawa da manema labarai, shugaban Gidaniyar, Malam Aliyu Sidi Attahiru ya koka ainun game da yanayin zamantakewa na Almajiri a Arewacin Najeriya.

A cewar sa lalle abin nada bukata ayi gyara akai.

Ahalinyanzu Gidauniyar ta Asattahir tana kokarin ta hada kai da Hukumomin Gwamnati don ganin an gudanarda cikakken nazari domin Samar da Nizami da kuma tsari domin kula da makarantun, da kuma kula da ingancin lafiyar yara musamman Almajirai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel