Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka miliyan 20 a zangon Buhari na 2 - Minista

Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka miliyan 20 a zangon Buhari na 2 - Minista

- Gwamnatin tarayya na shirin samar da ayyuka miliyan 20 a mulki Shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu

- Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Okechukwu Enelamah yace hakan na daga cikin kokarin gwamnatin na rage yawan rashin aiki

- Za a samar da ayyukan daga manyan ma’aikatun tattalin arziki hudu: Noma, gine-gine, sufuri da jukuma ma’aikatar ayyuka

Gwamnatin tarayya na shirin samar da ayyuka miliyan 20 domin rage yawan rashin aikin yi a mulki Shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu.

Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Okechukwu Enelamah, ya bayyana hakan a Abuja a jiya, Talata, 28 ga watan Mayu a wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da ayyuka wanda hukumar ITF ta shirya.

Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka miliyan 20 a zangon Buhari na 2 - Minista

Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka miliyan 20 a zangon Buhari na 2 - Minista
Source: Facebook

Ministan, wanda ya samu wakilcin sakataren din-din-dinna ma’aikatar, Sunday Edet Akpan, yace gwamnatin tarayya za ta samar da ayyukan daga manyan ma’aikatun tattalin arziki hudu: Noma, gine-gine, sufuri da jukuma ma’aikatar ayyuka.

Yace ma’aikatar ta umurci ITF da ta zo da mafita na samar da ayyukan miliyan 20 a bangarori hudun cikin shekaru hudu masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Anyi wa wani mutumi bulala 40 kan laifi shan mangoro a watan Ramadana

Darakta Janar na ITF, Sir Joseph Ari, yace hukumar ta cika yan Najeriya sama da 450,000 da sana’o’i sanan ta tallafawa dukkansu da kayayyaki aiki cikin shekaru biyu da suka gabata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel