Anyi wa wani mutumi bulala 40 kan laifi shan mangoro a watan Ramadana

Anyi wa wani mutumi bulala 40 kan laifi shan mangoro a watan Ramadana

- Ibrahim Ismail ya sha bulala 40 saboda sha Mangoro da rana tsaka a lokacin azumin Ramadana

- Laifin ya sama na sashi 370 na dokar jihar Jigawa

- Anyi masa bulalan ne a tsakiyar kasuwar Rigim bayan wata kotu ta karanto wa jama’a laifin da Ismail ya aikata

Wata kotu a Jigawa a ranar Talata, 28 ga watan Mayu ta yanke wa wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila hukuncin shan bulala 40 saboda karya azuminsa da yayi a bainar Jama’a ba tare da dalili ba kuma da rana tsaka.

Alkalin kotun, Safiyanu Ya’u ya yanke wa Isma’il wannan hukunci ne bayan hukumar Hisba ta kama shi yana shan mangoro baro-baro a bainar jama’a alhalin kowa na Azumi da gangan.

Anyi wa wani mutumi bulala 40 kan laifi shan mangoro a watan Ramadana

Anyi wa wani mutumi bulala 40 kan laifi shan mangoro a watan Ramadana
Source: UGC

Ya’u ya ce bisa ga shari’ar musulunci laifi ne babba mutumin dake da koshin lafiya ya ki yin azumin watan Ramadana ba koko ya karya haka kawai ba tare da wani dalili ba da shari’a ya tabbatar.

Laifin ya sama na sashi 370 na dokar jihar Jigawa.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashen Zamfara: Mutum 23 sun bakunci lahira a Garin Kauran-Namoda

Ya ce a dalilin haka za a yi wa Isma’il bulala 40 a bainar jama’a domin ya zama ma wasu darasi cewa hakan ba a yi wa addini wasa.

Yace za lallasa bayan Isma;ial a Kasuwa sannan za ayi shela kowa ya fito a taru a gani. Idan aka yi masa haka zai zama darasi ga duk wadanda ke wasa da aikin ibada musamman Azumi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel