Kashe-kashen Zamfara: Mutum 23 sun bakunci lahira a Garin Kauran-Namoda

Kashe-kashen Zamfara: Mutum 23 sun bakunci lahira a Garin Kauran-Namoda

Wasu ‘yan bindiga sun sake yin ta’adi a jihar Zamfara inda aka kashe sama da mutum 20 a wasu kauyuka. An kai wannan hari ne a jiya Talata 28 ga Watan Mayu kamar yadda mu ka samu labari.

Jaridar nan ta Daily Trust ta rahoto cewa wadannan Miyagu sun kai hari ne a wasu Kauyuka da su ka hada da Tunga da Kabaje da ke cikin Garin Sakiji a cikin karamar hukumar Kauran-Namoda.

An kai wannan munanan hari ne da kimanin karfe 5:30 na Asuba, inda ‘yan bindigan su ka shiga harbi ko ta ina a cikin wadannan Kauyuka. Wasu sun mutu ne bayan an rutsa su da harbi a gonakinsu.

Wadannan ‘yan bindiga sun zo ne a kan babur inji shugaban karamar hukumar Kauran Namoda watau Alhaji lawal Isa Abdullahi. Yanzu haka za a bizne wadannan mutane da aka kashe a makon nan.

KU KARANTA: Manyan abubuwan da Buhari ya kamata yayi a wannan karo

Kashe-kashen Zamfara: Mutum 23 sun bakunci lahira a Garin Kauran-Namoda

Kisan Iyalin wani ‘Dan bindiga ya jawo an yi barna a Zamfara
Source: Depositphotos

Wani Bawan Allah mai zama a wannan gari, Aliyu Yushau, ya bayyana abin da ya faru inda yace wasu ‘Yan sa-kai ne su ka tare wani babur da aka goyo Iyalin wani ‘Dan bindiga, kuma su ka kashe su.

Bayan kashe Iyalin wannan ‘Dan bindiga ne aka dira wannan gari ana ta faman kone-kone. Wannan mai babur da aka kama ya dade yana kai wa Miyagun da ke ta’adi bayanai a boye cikin dajin da su ke.

Mun samu labari cewa jami’an tsaro su na cikin wadannan Kauyuka inda su ke cigaba da sintiri a jiragen sama na yaki yanzu haka domin ganin an kawo zaman lafiya a cikin yankunan na jihar Zamfara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel