Taron rantsuwa: Jami’an FRSC akalla 2000 za su yi aiki yau a Abuja

Taron rantsuwa: Jami’an FRSC akalla 2000 za su yi aiki yau a Abuja

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga manema labarai, Ma’aikatan FRSC akalla 2000 za a jibge a cikin babban birnin tarayya Abuja a dalilin bikin rantsuwar da ake yi yau Laraba 29 ga Watan Mayu.

Wani babban jami’in hukumar FRSC masu kula da tituna a Najeriya, Mista Gora Wobin, ya bayyana cewa za a baza ma’aikata da za su lura hanyoyi a yayin da ake sake rantsar da shugabannin Najeriya.

Gora Wobin ya bayyana wannan ne a lokacin da yake hira da manema labarai a Abuja Ranar Talata. Wobin yake cewa sun shirya ma’aikatansu tsaf domin gyara hanya da kula da cinkoso a wannan rana.

Babban jami’in hukumar yake cewa:

“Mu na da labarin cewa jama’a za su zo tun daga wuraren da ke kusa da kuma nesa, don haka mu ka tsara yadda za ayi wannan aiki.”

Mista Wobin yace:

KU KARANTA: An yi fatali da shari’ar EFCC da wani na-kusa da Jonathan

Taron rantsuwa: Jami’an FRSC akalla 2000 za su yi aiki yau a Abuja

Jami’an FRSC za su yi aiki wajen rantsar da Shugaban kasa
Source: Depositphotos

“Mu na sa ran jama’a da-dama za su shigo Abuja don haka za mu tsare kan iyakokin Birnin.”

“Za mu yi amfani ne da ma’ikatan mu har 2000 da kuma jami’an sa-kai…kuma za mu ajiye motoci a kan hanya, sannan mu hukunta duk wadanda su ka sabawa dokokin hanya ta hanyar cin su tara”

Haka zalika Wobin yace:

“Duk motar da aka gani kusa da wajen taron na yau, za a dauke ta a matsayin barazana, don haka za a bincike ta kafin a janye ta.

A karshe, wannan babban jami’in na hukumar FRSC yace za su yi aiki da jami’an tsaro irin su ‘Yan Sanda wajen ganin an yi wannan biki hankali kwance ba tare da jama’a sun sabawa dokoki ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel