Ya kamata Buhari ya daina ganin laifin kowa, ya yarda ya gaza – inji Frank

Ya kamata Buhari ya daina ganin laifin kowa, ya yarda ya gaza – inji Frank

Wani fitaccen ‘dan gwagwarmayar siyasa a Najeriya kuma tsohon jagora na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Timi Frank, ya nemi shugaba Buhari ya rika ɗaukar nauyin gazawar sa a kan mulki.

Kwamared Timi Frank yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daina ganin kowa wajen laifin da gwamnatinsa tayi na gaza kawo wani sauyin kirki a rayuwar al’umma a cikin shekaru hudu.

Timi Frank ya bayyana wannan ne a wani jawabi da yayi Ranar Talata 28 ga Watan Mayu a Abuja, bayan shugaban kasar ya zargi Dr. Abubakar Bukola Saraki da Rt. Hon. Yakubu Dogara da rashin kishin ƙasa.

Frank yace bai kamata Buhari ya riƙa ƙoƙarin laɓewa da shugabannin majalisa ba, bayan gwamnatinsa ta jefa al’umma cikin halin ƙa-ƙa-ni ƙa-yi, domin kuwa shi jama'a su ka zaba ya riƙe madafan iko.

“Kai (Buhari) jama’a su ka zaba kayi aiki ba Saraki da Dogara ba. Aikin majalisa shi ne su kafa dokoki a kasa…”

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran na APC yake cewa kwan-gaba-kwan-baya da kuma lalaci da rashin sanin aikin shugaba Buhari ne ya jawo abubuwa su ka tabarbare ba wai ‘yan majalisa ba.

“…Duk shugaban da ya bar aikin da ke kan sa, ya tafi yana wasu gamabarwar, bai cancanci ya jagoranci al’umma ba”

KU KARANTA: Buhari yayi wata muhimmiyar ganawa ana shirin rantsar da shi

Ya kamata Buhari ya daina ganin laifin kowa, ya yarda ya gaza – inji Frank

Timi Frank ya kare shugabannin Majalisa daga zargin Buhari
Source: Depositphotos

Frank ya cigaba da jawabi:

“Idan a yanzu bayan shekaru a kan mulki, shugaba Buhari bai da aikin yi sai kokarin daura nauyin zargi a kan wasu Bayin Allah na-dabam, yaushe zai fahimci cewa a yau Najeriya ta zama Matattarar Matsiyata a Duniya?”

Kwamared Frank ya kuma ce wannan gwamnatin APC ba ta iya samawa al’umma aikin yi ba, sai dai ma tattalin arzikin da ya shiga wani hali a dalilin munanan aƙidun tattalin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan Bawan Allah ya kuma ɗaura laifin ɓata lokacin da ake samu wajen sa hannu a kan kasafin kuɗin Najeriya a kan makarar da Buhari yake yi wajen miƙawa majalisa kundin kasafin a duk shekara.

A daidai lokacin da ake da’awar cewa Buhari mutum ne mai gaskiya, sai aka ji Malaman jami’a su na kukan ya sabawa alkawarin da ya dauka. Haka kuma Mai dakinsa ta fito tana kuka da gwamnatinsa, inji Frank.

Wani Tsohon Jigon APC yayi kaca-kaca da Shugaba Buhari bayan ya soki shugabannin Majalisa. Timi Frank yace Buhari ya jefa jama’a cikin halin Ni-‘Ya su ba Majalisa ba don haka yace a daina ɗaurawa wasu laifi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel