Operation halaka dodo: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma yan ta’adda kisan gilla a Borno

Operation halaka dodo: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma yan ta’adda kisan gilla a Borno

Zaratan dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya dake aikin Operation halaka dodo a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar halaka wasu mayakan Boko Haram a garin Gwoza na jahar Borno ta hanyar yi musu kisan gilla.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan kasa, kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu yayin wani arangama tsakanin Sojoji da yan ta’adda a lokacin da suka yi kokarin tsallakewa zuwa dajin Sambisa.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta yi caraf da kanin sakataren gwamnatin Zamfara dauke da naira miliyan 60

Kanal Sagir yace a sakamakon musayar wutar da aka yi, Sojoji sun bindige yan ta’adda guda biyu, inda nan take suka fadi matattu, sa’annan ya kara da cewa “Muna cigaba da gudanar da aikin Operation halaka dodo a yankin.

“Muna gudanar da wannan aiki ne domin hana yan ta’adda wani katabus, tare da takuresu ta yadda ba zasu damar zirga zirga ba a wannan yanki, balle ma har su yi tunanin kaddamar da hare hare.” Inji shi.

Wasu daga cikin kayayyakin da Sojojin suka gano daga wajen yan ta’addan sun hada da makamai da kuma nau’o’in magunguna daban daban da zasu kai ma sauran yan ta’addan da suka yi kaka gida a cikin dajin.

Shima kwamandan rundunar Soji ta 7 dake Borno, Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu ya jinjin ma Sojojin saboda jarumtar da suka nuna, sa’annan ya basu tabbacin samun goyon baya daga babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel