Buhari ya kankaro Najeriya, ya cika alkawarin da FG ta daukar wa Westerhof a 1994 (Hotuna)

Buhari ya kankaro Najeriya, ya cika alkawarin da FG ta daukar wa Westerhof a 1994 (Hotuna)

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara farfado da kimar Najeriya a idon duniya bayan ta cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta daukar wa tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta kasa (Super Eagles), Clemens Westerhof, na bashi gida domin nuna jin dadin nasarar da ya jagoranci 'Super Eagles' ta samu.

Clemens Westerhof, ne mutumin da ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta kasa, 'Super Eagles' har ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika sannan ya kai kungiyar a karo na farko zuwa gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.

Saboda wannan kokari da ya yi sai gwamnatin tarayya ta dauki alkawarin bashi kyautar amma sai hakan ta gagara.

Buhari ya kankaro Najeriya, ya cika alkawarin da FG ta daukar wa Westerhof a 1994 (Hotuna)

Westerhof da mukarraban gwamnatin Buhari
Source: Twitter

Buhari ya kankaro Najeriya, ya cika alkawarin da FG ta daukar wa Westerhof a 1994 (Hotuna)

Fashola da Westerhof a fadar shugaban kasa
Source: Twitter

Buhari ya kankaro Najeriya, ya cika alkawarin da FG ta daukar wa Westerhof a 1994 (Hotuna)

Fashola ke mika wa Westerhof takardar mallakar gida
Source: Twitter

A ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, 2019, ne gwamnatin Buhari ta cika wannan alkawari da Najeriya ta dauka, shekaru 25 da ta wuce.

Ministan aiyuka, gidaje da lantarki, Babatunde Fashola, ya mika takardar shaidar mallakar gida ga Weterhof a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel