Bayan shekaru 4 mulki, babu wani sabon abun da Buhari ya mallaka - Fadar shugaban kasa

Bayan shekaru 4 mulki, babu wani sabon abun da Buhari ya mallaka - Fadar shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika takardun jerin dukiyoyin da ya mallaka ga cibiyar ladabin ma'aikatan gwamnati wato Code of Conduct Bureau (CCB).

Bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya, wajibi ne shugaban kasa ya sallama takardan kafin rastar da shi da za'ayi a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2019.

A wani jawabi da mai magana da yawun shugaba kasa, Garba Shehu ya saki, ya ce shugaba Buhari ya cika takardan kuma babban hadimin shugaban kasa kan harkokin gida, Sarki abba, ya kaiwa shugaban cibiyar CCB, Farfesa Mohammad Isa, a madadin shugaba Buhari.

Yace: "Takardun, kamar yadda Shugaba Buhari ya rattaba hannu kuma ya rantse gaban babban kotun Abuja ya nuna cewa babu wani muhimmin canji da takardar na shekaran 2015."

"Babu Sabbin gidaje, babu sabbin asusun banki a gida da waje, babu wasu sabbin hannun jari."

Ya ce shugaban CCB ya yabawa shugaban kasa kan wannan abu da yayi na bayyana dukiyoyinsa bisa doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel