Rantsar da Buhari: Jerin hanyoyi 12 da rundunar 'yan sanda zata rufe a Abuja

Rantsar da Buhari: Jerin hanyoyi 12 da rundunar 'yan sanda zata rufe a Abuja

Rundunar 'yan sanda a Abuja ta bayyana cewar zata rufe wasu hanyoyin zuwa filin taro na 'Eagle Square', wurin da za ai bikin sake rantsar da Buhari a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu a ranar Laraba.

Mataimakin kwamishinan rundunar 'yan sandan Abuja mai kula da atisaye, DCP Usman Umar, ne ya sanar da haka a ranar Talata yayin wani taro da manema labarai a hedikwatar rundunar 'yan sandan Abuja.

Ya bayyana cewar rundunar 'yan sanda tare da hadin gwuiwar ragowar hukumomin tsaro zasu tabbatar da cewar an yi taron rantsuwar an gama lafiya.

Ya kara da cewa rufe hanyoyin da zasu sada jama'a da filin taro na 'Eagle Square' na daga cikin matakan tsaron da suka dauka domin ganin al'amura sun gudana cikin kwanciyar hankali.

Rantsar da Buhari: Jerin hanyoyi 12 da rundunar 'yan sanda zata rufe a Abuja

Buhari yayin rantsar da shi a shekarar 2015
Source: UGC

Hanyoyin da abin zai shafa sun hada da: titin Aso Drive, FCDA daura da hedikwatar ma'aikatar kudi, kwanar gidan gwamnatin jihar Bayelsa, hanyar zuwa zauren majalisa, kwanar Gana da zata bulle zuwa Transcorp , kwanar titin Ahmadu Bello da zata bulle zuwa Nitel , titin Kura Mohammed daura da Benue House Plaza, NNPC Tower, titin karkashin gadar Federal Sec Phase III, titin karkashin gadar dake bayan ma'aikatar harkokin kasashen waje, titin zuwa FCDA daura POWA da babban titin Goodluck Ebele Jonathan (wanda ya zarce mahadar 3 Arm Zone).

DUBA WANNAN: Kotu ta haramta kama hadiman sarkin Sanusi II

"Mu na masu bawa jama'a hakurin matsin da zasu iya fuskanta sakamakon rufe hanyoyin tare da basu shawarar su yi amfani da wasu hanyoyin domin zuwa wuraren da suke so," a cewar DCP Umar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel