'Yan sanda sun fara binciken mutuwar hadimin Gwamna Shettima a gidan gwamnati

'Yan sanda sun fara binciken mutuwar hadimin Gwamna Shettima a gidan gwamnati

A ranar Talata 28 ga watan Mayu ne misalin karfe 2:30 na rana aka tsinci gawar John Achagwa rataye a kan bishiya a bayan masaukin shugaban kasa da ke gidan gwamnatin jihar Borno.

Achagwa mai matsakaicin shekaru ma'aikaci ne a gidan gwamnatin jihar Borno.

Kwashinan 'yan sandan jihar, Mohammed Aliyu ya tabbatar da rasuwarsa kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

A cewar Aliyu, babu wata alamar cewa marigayin yana fama da wata damuwa saboda haka zai yi wahala a iya hasashen abinda dalilin abinda ya yi kama ta shi ne ya kashe kansa.

'Yan sanda sun fara binciken mutuwar hadimin Shettima a gidan gwamnati

'Yan sanda sun fara binciken mutuwar hadimin Shettima a gidan gwamnati
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame

Domin haka, ya ce akwai bukatar a zurfafa bincike a kan lamarin domin gano ainihin dalilin da ya yi sanadin afkuwar lamarin.

Ya kuma shaidawa wa majiyar Legit.ng cewa abokan aikin Achagwa sun ce sun lura da alamun kamar akwai abinda ke damunsa duk da cewa baya rikici da kowa kuma mutum ne mai saukin kai.

A cewarsu, yana korafi kan wasu matsaloli na iyali.

Kafin afkuwar lamarin, an ce ya taho wurin aiki amma baya anashuwa amma bayan ya yi alwala na sallar Azahar ba a sake ganinsa ba.

Daga bisani sai aka gano gawarsa a rataye a bishiya a bayan masaukin shugaban kasa na gidan gwamna.

An sako da gawarsa daga bishiyar bayan sa'a guda domin a kai shi zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibiti.

Marigayin ya yi aiki da gwamnatoci da yawa na mulkin soji da farar hula.

Duk da cewa ya yi murabus daga aiki yayin mulkin Shettima karo na biyu, gwamnan ya nemi ya cigaba da aiki saboda kwarewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel