Ni na shawo kan Dino Melaye ya fasa kashe kansa - Shaida ya fadawa kotu

Ni na shawo kan Dino Melaye ya fasa kashe kansa - Shaida ya fadawa kotu

- Saja Alwo Mohammed ya ce shine ya roki Sanata Dino Melaye kada ya kashe kansa

- Ana zargin Sanata Melaye ne da aikata laifuka shida masu alaka da yunkurin kashe kansa

- Mohammed ya ce Melaye ya fasa gilashin motar da ke dauke da shi daga Abuja zuwa Lokoja

Wani shaida ya fadawa alkalin kotu babban birnin tarayya Abuja cewa shine ya roki Sanata Dino Melaye kada ya sha wani abin sha da ke hannunsa ranar da ya yi ikirarin zai kashe kansa a ranar 24 ga watan Afrilun 2018.

A yayin da ya ke bayar da shaida, Dan sandan, Saja Alwo Mohammed ya ce: "Na roki shi ya koma cikin mota. Na fada masa shine Sanatan da na fi kauna. Amma bai tashi ba. Yana rike da wani abu a hannunsa."

Ni na roki Dino Melaye kada ya kashe kansa - Shaida ya fadawa kotu

Ni na roki Dino Melaye kada ya kashe kansa - Shaida ya fadawa kotu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun fara binciken mutuwar hadimin Gwamna Shettima a gidan gwamnati

An gurfanar da Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta Yamma ne gaban Mai shari'a Sylvanus Orji na babban kotu da ke zamanta a Apo inda kae tuhumarsa da aikata laifuka shida ciki har da yunkurin kashe kansa, yunkurin tserewa daga hannun 'yan sanda da barnata kayan gwamnati.

Ana zarginsa da aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Afrilun 2018 yayin da 'yan sanda suke hanyarsu na tafiya da shi Lokoja na jihar Kogi.

Ya ce, wanda ake tuhumar da laifin ya fasa gilashin mota, ya mike tsaye da fara ihu cewa, "Ba zan tafi Lokoja ba."

A cewarsa, ya rike shi da hannu daya. "Yayin da muke kokarin rike wanda ake zargin, ya tura daya daga cikin jami'an 'yan sanda ya bude kofa. Sannan ya daka tsalle ya fito daga motar ya zauna a kasa ya fara ihun cewa zan kashe kai na in jefa 'yan sanda cikin fitina."

Mai bayar da shaidan ya kara da cewa daga nan ne wasu 'yan daba suka tare motar suka karbe Melaye suka tafi da shi cikin mota.

Sajan 'dan sandan ya ce sun bi motar 'yan daban kuma suka kama su a Yar'Adua Centre.

"Mun kama su kusa da Yar'Adua centre saboda motarsu ya yi hatsari da wata Jeep. Wasu daga cikin mutanen sun tsere sai dai munyi nasarar cafke guda daya."

Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 11 da 18 ga watan Satumba da ranar 3 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel