Badakkalar N57m: Bani da wata matsala da ku, mahaifiyar Maryam Sanda ta fadawa kotu

Badakkalar N57m: Bani da wata matsala da ku, mahaifiyar Maryam Sanda ta fadawa kotu

-Maimuna Aliyu tace ita ba tada ta cewa zargin da ake mata na almundahanar N57m.

-Hukumar ICPC ce ta shigar da karar akan laifuka guda uku da take tuhumar mahaifiyar Maryam Sanda da aikatawa.

Tsohuwar daraktar Aso Loans and Savings Maimuna Aliyu ta fadawa babban kotun kasa ta Abuja cewa babu abinda zata ce dasu akan badakkalar N57m da aka danganta ta dashi.

Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda wacce itama ke gaban shari'a sakamakon zarginta da akeyi da laifin kisan mijinta, ta tsinci kanta a kotu. Hukumar yaki da cin hanci da sauran laifuka masu alaka da cin hancin ta ICPC ce tayi kararta akan laifuka uku da ake zarginta da aikatawa.

Badakkalar N57m: Bani da wata matsala da ku, mahaifiyar Maryam Sanda ta fadawa kotu

Badakkalar N57m: Bani da wata matsala da ku, mahaifiyar Maryam Sanda ta fadawa kotu
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Zan zarce tare da wasu daga cikin ministocina, inji Buhari

Laifi na farko kamar yadda yake kunshe cikin kararar da aka shigar shine, ana zarginta da sayar da fuloti uku na fili a shiyar Jabi District dake Abuja kan N57m a madadin bankin da take aiki ba tare da ta baiwa bankin ko kobo ba.

Abu na biyu shine, tayi wa hukumar ICPC karya ta hanyar cewa ta baiwa wani ma’aikacin bankin kudin domin ya sanya cikin asusun bankin alhali kuma ta san karyata ke. Hakan ma ya sanya aka bayar da belinta a wancan lokacin.

Yayin da ake cigaba da sauraron karar a ranar Talata, shugaban tawagar lauyoyin dake kare ta, Muhammad Monguno ya roki kotun da tayi watsi da karar akan dalilin rashin shigar da karar ba’a bisa ka’ida ba sannan kuma ta sallami Maimuna ta hanyar wanke ta daga zargi.

A bangare guda kuwa, lauyan dake jagorantar shigar da wannan kara, Osuobeni Akponishisingha ya fadawa kotun cewa wannan magana da Maimuna tayi sam ba ta da makama bare tushe. Idan har kotu na da bukatar wani shaida to zai gabatar da Mista Hassan tsohon babban daraktan Aso Savings domin yazo ya gabatar da shaida.

Jastis Mairo Nasir, wacce ke shari’ar ta dage sauraron wannan karar zuwa lokacin da bata sanya rana ba amma dai zata sanar da bangarorin biyu nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel