Kakakin Majalisar Imo ya yi murabus

Kakakin Majalisar Imo ya yi murabus

Kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Acho Ihim, ya yi murabus daga kujerar sa ta kakakin majalisa a ranar Talata. Honarabul Acho ya yi murabus daga kujerar sa ta jagoranci da misalin karfe 5.25 na Yammacin Talata.

Kakakin Majalisar Imo ya yi murabus

Kakakin Majalisar Imo ya yi murabus
Source: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, sauka daga kujerar jagoranci bai takaita kadai akan kakakin majalisar ba yayin da mataimakin sa, Ugonna Uzuigbo da kuma shugaban majalisar mai rinjaye, Lugard Osuji suka bi sahun sa.

Murabus din Honarabul Acho da sauran manyan 'yan majalisar biyu na zuwa ne awanni ashirun da hudu bayan da wa'adin tsige sa daga kujerar sa ta jagoranci ya kare.

A baya an kai ruwa rana tsakanin 'yan majalisar guda 21 da kuma kakakin majalisar yayin da suka bangare tare da hura masa wutar sauka daga kujerar sa bisa jagorancin Honarabul Chinedu Offo dake hankoron maye gurbin sa.

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya bayyana kadarar sa yayin gabatowar ranar rantsuwa

Cikin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, yayin da a gobe Laraba, 29 ga watan Mayun 2019 ta kasance ranar Dimokuradiyya, da yawa daga cikin gwamnonin Najeriya sun sauke dukkanin 'yan majalisar gwamnatin su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel