Kotu ta haramta kama hadiman sarkin Sanusi II

Kotu ta haramta kama hadiman sarkin Sanusi II

A ranar Talata, 28 ga watan Mayu, ne wata kotun majistare a jihar Kano ta bayar da umurin damke wasu ma'aikatan masarautar Kano su uku, wanda ya hada da Mannir Sanusi, shugaban ma'aikatan fadar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano (PCAC) ta shigar da karar mutane ukun ne bayan sun ki bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi da bayar da bayani a kan zargin badakala da kudin masarauta da ake yiwa fadar sarkin Kano, karkashin mai martaba, sarki Sanusi II.

Sai dai, wata babbar kotu a jihar Kano karkashin mai shari'a Suleiman Baba Namalam ta bayar da umarnin haramta wa hukumar yaki da cin hancin kama mutanen uku. Kotun tayi wannan hukunci bayan lauyan hadiman sarkin, Barista A. B Mahmoud ya garzaya gaban kotun da kokon barar sa. Kazalika, ya daga sauraron karar zuwa 13 ga watan Yuni.

Kotu ta haramta kama hadiman sarkin Sanusi II

Sarkin Sanusi II
Source: Twitter

Amma shugaban hukumar PCAC, Muhyi Magaji, ya ce bai da masaniya a kan sabon umarnin haramta wa hukumar da yake jagoranta kama ma'aikatan masarautar ta Kano.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano tana shirin garkame Alhaji Munir Sanusi, shugaban ma'aikatan sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a kan rashin gurfana gaban hukumar domin amsa tambayoyi.

Kana za'a damke wasu ma'aikatan masarautar Kano biyu, Mujitaba Abba Sani da Sani Muhammad Kwaru, wadandan sukayi kunnen kashi kan gayyatar da hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yiwa sarkin Kano na badakalar N4bn.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel