Gwamna Ganduje ya bayyana kadarar sa yayin gabatowar ranar rantsuwa

Gwamna Ganduje ya bayyana kadarar sa yayin gabatowar ranar rantsuwa

Kotun da'ar da ma'aikata reshen jihar Kano na sake tunatar da dukkanin zababbu da masu nadin mukamai na siyasa da su bayyana dukiyoyi da kadarorin da suka mallaka kamar yadda doka ta tayi tanadi ko kuma su fuskanci hukunci.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje
Source: Twitter

Shugaban babbar kotun na jihar Kano, Umar Saulawa, shi ne ya bayar da wannan umurni a wata hira yayin ganawar sa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa cikin birnin Kano a ranar Talata.

A cewar sa, kotun ba za ta yi sassauci ba wajen daukar hukuncin da ya dace ga duk wani dan siyasa da ya sabawa wannan umurni kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Saulawa yayin yiwa umurnin sa tozali, ya ce tuni gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dukkanin kadarori da kuma dukiya da ya mallaka bayan kammala wa'adin gwamnatin sa na farko da kuma gabanin fara wa'adin gwamnatin sa na biyu.

KARANTA KUMA: Hadimin gwamna Kashim ya kashe kansa a fadar gwamnatin Borno

A yayin da a gobe Laraba, 29 ga watan Mayun 2019 za a rantsar da gwamna Ganduje bisa kujerar jagoranci ta gwamnatin Kano a wa'adin na biyu, shugaban kotun da'ar ma'aikatan ya ce bayyana kadarar da gwamna Ganduje yayi ya dace da tanadin shari'a cikin kundin tsarin mulki na kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel