INEC ta fara bitar zabukan 2019

INEC ta fara bitar zabukan 2019

-Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fara gudanar da bita akan zaben 2019 domin gano inda matsala take sannan ayi shirin gyarata.

-An fara gudanar da wannan taron bitar ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja, kamar yanda shugaban hukumar ya fadi.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta fara gudanar da bita akan zabukan 2019 domin sake inganta shiri saboda zabukan dake tafe nan gaba.

Shugaban hukumar ta INEC farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya bayyanawa manema labarai cewa hukumarsa ta fara zaman bitar zaben 2019 a Abuja ranar Talata.

INEC ta fara bitar zabukan 2019

INEC ta fara bitar zabukan 2019
Source: Getty Images

KU KARANTA:Zan zarce tare da wasu daga cikin ministocina, inji Buhari

A cewarsa ganawar ranar Talata ita ce ta farko tun bayan kammala zabe, kana kuma ta farko bayan zama da sukayi domin samun matsaya akan yadda za’a gudanar da zaben 2019.

Yakubu yace, yana fatan duk abubuwan da aka tattauna wurin bitar zasuyi wa hukumar amfani domin sake inganta yanayin gudanar da zabukan kasar nan.

Bugu da kari, hukumar zatayi wawaye adon tafiya ta hanyar binciko korafe-korafe da suka shafi irin wannan zaman nasu tun shekaru 40 da suka gabata. Akwai na Babalakin wanda akayi a shekarar 1986, rahoton Uwais a shekarar 2008, kwamiti na Lemu akan rikicin bayan zabe a shekarar 2011 sai kuma kwamitin Nnamani akan yiwa dokokin zabe garambawul na shekarar 2017.

A wani labari mai kama da wannan, mun ji cewa wani masanin tattalin arziki yace akwai kwararan dalilan da kan iya sa shugaba Buhari ya janye tallafin man fetur.

David Ibidapo yace janye tallafin man shi ne zai bawa gwamnati damar aiwatar da kasafin kudin 2019 tare da samun damar biyan mafi karancin albashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel